Najeriya

Al'ummar Ondo na zaben sabon gwamna

Al’ummar Ondo a tarayyar Najeriya na kada kuri’a a zaben kujerar gwamnan jihar, inda ‘yan takara 17 ke fafatawa, a kananan hukumomi 18.

Takardar kada kuri'a a zabukan Najeriya.
Takardar kada kuri'a a zabukan Najeriya. Reuters
Talla

'Yan takarar da suka fi shahara dai sun hada gwamna mai ci na jam’iyyar APC Rotimi Akeredolu, Eyitayo Jegede na jam’iyyar PDP sai kuma Agboola Ajayi na jam’iyyar ZLP.

Gabannin zaben kasa da sa’o’i 48, jam’iyyar PDP tace ba ta amince da Eyitope Ogunbode shugaban jam’I’ar Obafemi Owolowo a matsayin wanda zai jagoranci zaben na Ondo ba, saboda kusancinsa da gwamna mai ci Rotimi Akeredolu.

Sai dai yayin zantawa da sashin Hausa na RFI, mai Magana da yawun hukumar zaben, Nick Dazan yayi watsi da zargin na PDP, inda ya ce sai a yau, wato ranar zaben ne za su bayyana babban jami’in da zai jagoranci zaben gwamnan na Ondo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI