Gwamnan Bauchi ya nemi Sarkin Misau ya rubuto wasikar neman yafiya
Gwamnatin Jihar Bauchi da ke Najeriya ta bukaci mai martaba sarkin Misau, Alhaji Ahmed Suleiman da ya rubuta wasikar neman gafara saboda samun sa da hannu a rikicin da akayi tsakanin manoma da makiyaya a karamar hukumar wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 11.
Wallafawa ranar:
Wannan ya biyo bayan shawarwarin rahotan kwamitin da gwamnatin jihar Bauchi ta kafa, kamar yadda sanarwar da Mukhtar Gidado mataimaki na musamman ga Gwamna Bala Muhammad kan harkokin yada labarai ya gabatar, inda gwamnatin ta kuma bukaci hukunta wasu masu rike da sarautun gargajiya a karamar hukumar.
Sanarwar gwamnatin tace Gwamnan ya amince da shawarwarin da kwamitin ya gabatar wadanda suka hada da bukatar Sarkin Misau ya nemi gafara a rubuce saboda ruru wutar rikicin.
Sanarwar ta bukaci Masarautar Misau da ta gagaguta warware rawanin Ibrahim Yusuf Atiku a matsayin Wakilin Zadawa, yayin rahotan ya bukaci kwamishinan shari’a da ya hada kai da kwamishinan Yan Sanda wajen gurfanar da Atikun a gaban kotu saboda hannu dumu dumu kan raba gandun daji da kuma karbar cin hanci da rashawa.
Gwamnatin Jihar Bauchin ta kuma sanar da yiwa Daraktan mulki Malam Sule Abba da Daraktan noma da albarkatun kasa Malam Baba Waziri da Daraktan ayyuka Aminu Abdullahi Disina na karamar hukumar Misau ritaya daga aiki.
Kwamitin ya bada shawara sake bincike kan wasu mutane 16 da ake zargin suna da hannu cikin rura wutar rikicin, yayin da aka dakatar da Hakimin Chiroma, Alhaji Ahmadun Amadu daga aiki har sai bayan kamala bincike.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu