Najeriya

Matasa na ci gaba da zanga-zangar neman rusa rundunar SARS a Najeriya

Wasu masu zanga-zanga a Najeriya.
Wasu masu zanga-zanga a Najeriya. AFP PHOTO

Daruruwan matasa ne yau suka cigaba da zanga zanga a birnin Lagos dake Najeriya inda suke bukatar rusa rundunar Yan Sandan dake yaki da fashi da makami da ake kira SARS da kuma bukatar ganin an hukunta wadanda ake zargi da laifi daga cikin su.

Talla

Masu zanga zangar a sassan birnin Lagos sun yi gangami tare da yin tattaki dauke da allunan dake da rubuce rubuce domin bayyana fushin su da sashen Yan Sanda da suka ce yayi kaurin suna wajen cin zarafin jama’a da kwace musu dukiyoyi da kuma kisan gilla.

Rahotanni sun ce an gudanar da zanga zangar cikin kwanciyar hankali a Edo da Lagos da Oyo, yayin da aka fuskanci tashin hankali a Osogbo da Delta da Abuja, wanda ya kaiga kasha dan sanda guda a Jihar Delta.

Wannan zanga zangar dai ta samu goyan bayan fitattun mutane wadanda ke nema yiwa sashen Yan sandan garambawul saboda korafe korafen da ake yi akan su.

Cikin wadanda suka bayyana damuwa dangane da koke koken sun hada da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki tare da kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Amnesty International.

Idan dai ba’a manta ba, Sufeto Janar na Yan Sandan Najeriya Adamu Muhammad ya baiwa sashen rundunar ta SARS umurnin daina tare hanya suna gudanar da bincike kan jama’a sakamakon irin wadannan zarge zarge masu yawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI