Najeriya-Kano

Ganduje ya kori hadiminsa saboda sukar Buhari

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Solacebase

Gwamnan Jihar Kano da ke Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya dakatar da mai bashi shawara kan harkokin yada labarai Salihu Tanko Yakasai daga aiki saboda sukar shugaban kasa Muhammadu Buhari a kafar sada zumunta.

Talla

Kwamishinan yada labaran Jihar Muhammad Garba ya sanar da dakatar da Yakasai a cikin wata sanarwar da ya rabawa manema labarai wadda ke kushe da matakin Gwamnan.

Kwamishinan yace duk da yake Yakasai ya amsa yin kalaman da ake zargin sa wanda ya bayyana su a matsayin na kashin kan sa ne, yana da wahala jama’a su banbance saboda ganin yadda yake rike da mukamin gwamnati.

Gwamna Ganduje ya kuma gargadi masu rike da mukaman gwamnati da su kaucewa yin kalaman dake tada hankali, yayin da ya jaddada goyan bayan sa ga jagoranci da kuma shirye shiryen shugaban kasa Muhammadu Buhari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.