Najeriya ta rushe rundunar SARS mai yaki da fashi da makami
Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Muhammadu Adamu ya sanar da rusa rundunar da ke yaki da 'yan fashi da makami da ake kira SARS, sakamakon zanga zangar da aka gudanar saboda kaucewa ka’idar aiki.
Wallafawa ranar:
Babban Sufeton yayin wani jawabin kai tsaye ta gidan talabijin mallakin kasar, ya amsa kiran 'yan Najeriyar wajen rusa sashen rundunar ‘yansandan na musamman mai yaki da fashi da makami, yayinda ya bukaci gaggauta janye ilahirin jami'an na SARS da yanzu haka ke bakin aiki.
Mutane da dama da sun bayyana bacin ran su da yadda wasu batagari dake cikin rundunar ke azabtar da jama’a da raba su da dukiyoyin su da kuma kisa a wasu lokuta.
Al'ummar kasar dai sun shafe kwanaki suna zanga-zangar bukatar kawo karshen rundunar ta SARS wadda ta samu goyon bayan fitattu daga sassa daban-daban.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu