Najeriya

Rotimi Akeredolu na Jam'iyyar APC ya sake lashe zaben jihar Ondo

Jam'iyyar APC a Najeriya ta lashe zaben Gwamnan Jihar Ondo da aka yi a jiya Asabar inda Gwamna mai ci Rotimi Akeredolu ya samu kuri’u 292,830 sabanin abokin karawar sa na PDP Eyitayo Jegede da ya zo na biyu da kuri’u 195,791.

Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu.
Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu. Twitter/@RotimiAkeredolu
Talla

Rahotanni daga masu sa ido a zaben sun nuna cewar an yi ta sayen kuri’u daga kowanne bangare na Jma’iyyun da suka shiga takara.

Baturen zabe kuma mataimakin shugaban Jami’ar Ibadan, Farfesa Abel Idowu Olayinka ya bayyana sakamakon a Akure.

Tuni shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aike da sakon taya murna ga Gwamna Akeredolu inda ya bukace shi da ya dada jajircewa wajen yi wa jama’a aiki fiye da wanda ya yi a wa’adin sa na farko.

Buhari ya kuma yabawa masu kada kuri’u a Jihar Ondo kan yadda aka yi zaben cikin kwanciyar hankali, yayin da ya bayyana gamsuwar sa dangane da rawar da jami’an tsaro suka taka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI