Najeriya-Ondo

Zaben Ondo: Gwamna Akeredolu ya baiwa abokan hamayyarsa tazara

'Yan Najeriya na cigaba da dakon sakamakon zaben gwamnan jihar Ondo da ya gudana a ranar asabar 10 ga watan Oktoba, wanda mutane da dama suka fita don kada kuri’unsu.

Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu
Gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu Twitter/@RotimiAkeredolu
Talla

‘Yan takara 17 ne suka fafata a zaben, sai dai hammaya ta fi zafi tsakanin gwamna mai ci na jam’iyyar APC Rotimi Akeredolu, da Eyitayo Jegede na PDP, sai kuma Agboola Ajayi na jam’iyyar ZLP.

Sai dai rahotanni sun ce sakamakon da aka soma tattarawa ya nuna gwamna mai ci Rotimi Akeredolu ke kan gaba tsakanin 'yan takarar.

Sa’o’I bayan kammala kada kuri'u, kwamishiniyar hukumar zabe a jihar ta Ondo, Farfesa Anthonia Simbine ta shaidawa manema labarai cewa, sun samu nasarar dora akalla kashi 75 na sakamakon kuri’un da aka kada zuwa shafinsu na Intanet, sai dai babu tabbacin lokacin da za su kammala kidayar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI