Najeriya

'Wasu tsiraru ne ke danne kudin yaki da Boko Haram'

Kungiyar Transparency International tare da hadin guiwar CISLAC mai fafutukar tabbatar da gaskiya a Najeriya, ta zargi wasu jiga-jigan sojojin kasar da karkatar da kudaden da aka ware domin yaki da matsalolin tsaro da suka hada da rikicin Boko Haram da hare-haren ‘yan bindiga da kuma sace-sacen jama’a domin karbar kudin fansa.

Mayakan Boko Haram
Mayakan Boko Haram AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Bayan binciken da suka gudanar, kungiyoyin biyu sun ce, sojojin kasar sun sha mika kokensu ga gwamnatin tarayya don ganin cewa, ainihin kudaden da ake ware wa bangaren tsaro a kasafi sun iso hannayen da suka dace.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da Abdurrahman Gambo Ahmad ya yi da shugaban Transparency International a Najeriya kuma jigo a CISLAC, Auwal Ibrahim Musa Rafsanjani.

Hira kan almundahanar sojojin Najeriya tare da Auwal Musa Rafsanjani

Har yanzu jami'an tsaron Najeriya sun gaza shawo kan matsalolin tsaron da suka yi wa kasar dabaibayi, lamarin da ya sa wasu masana lamurran tsaro ke diga ayar tambaya kan ikirarin gwamnatin kasar na yaki da ta'addanci da satar jama'a da kuma hare-haren 'yan bindiga.

Bayanai sun nuna cewa, akwai wasu tsirarun mutane da ke yi wa bangaren tsaro zagon-kasa kamar yadda Kungiyar Transparency International ta bayyana.

Masana lamurran tsaro sun ce, muddin za a ci gaba da yi wa bangaren tsaro zagon kasa, to babu shakka kasar za ta ci gaba da fuskantar koma-baya a fafutukarta ta tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a fadin Najeriya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI