Bakonmu a Yau

'Yan fashi na murna da rusa rundunar SARS- Tsohon Babban Sufeton 'Yan sanda

Wallafawa ranar:

A yayin da al'ummar Najeriya ke ci gaba da cece-kuce game da rusa sashen rundunar 'yansanda na musamman mai yaki da fashi da makami wanda aka fi sani da SARS, tsohon Sufeta Janar na 'yan sandan kasar, Sulaiman Abba ya bayyana cewa, miyagun 'yan fashi da makami da masu satar jama'a na murna da matakin, abin da su ke ganin zai ba su damar cin karensu babu babbaka.Alhaji Abba wanda ke bayyana hakan yayin zantawarsa da sashen Hausa na RFI, ya ce miyagun sun fi fargabar yin gaba da gaba da dakarun SARS fiye da 'yan sanda zalla.

A karshen makon da ya gabata ne, Babban Sufeton 'yansandan Najeriya Muhammadu Adamu ya amince da rushe rundunar ta SARS bayan tsanantar zanga-zanga.
A karshen makon da ya gabata ne, Babban Sufeton 'yansandan Najeriya Muhammadu Adamu ya amince da rushe rundunar ta SARS bayan tsanantar zanga-zanga. amnesty international
Sauran kashi-kashi