Najeriya

An kafa sabuwar rundunar SARS a Najeriya

Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu
Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu Vanguard.ng

Babban Sufeta Janar na 'yan sandan Najeriya Muhammadu Adamu ya sanar da kafa sabuwar runduna mai suna SWAT wadda za ta maye gurbin SARS mai yaki da ‘yan fashi da makami da aka rusa.

Talla

Sanarwa da ofishin Adamu ya fitar, ta ce jami’an da za a tura wannan sabuwar rundunar za su fuskanci gwaje-gwaje da suka hada da na kwakwalwa da lafiyarsu kafin a tura su cibiyoyin samun horo nan da makon gobe.

Adamu ya ce jami’an da za a dauka daga kudancin kasar domin aiki a wannan sashe za su samu horo a Cibiyar Horar da 'Yan Sandan da ke yaki da ‘yan ta’adda a Nonwa-Tai ta jihar Rivers, yayin da wadanda za su fito daga arewacin Najeriya za su samu horo a Kwalejin 'Yan Sanda da ke Ende a jihar Nasarawa.

Sanarwar ta ce wadanda suka fito daga yankin yammacin Najeriya za su samu horo ne a Ila-Orangun da ke Jihar Osun.

Sufeto Janar din ya bukaci jami’an da suka yi aiki a tsohuwar rundunar SARS da aka rusa da su kai kansu Cibiyar 'Yan Sandan da ke Abuja domin ganawa da su da kuma tantance lafiyarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI