Najeriya

Mu dai Buhari ka dawo mana da SARS- 'Yan Borno

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Nigeria/presidency

Kungiyoyin fararen hula sun gudanar da zanga-zanga a birnin Maiduguri na jihar Bornon Najeriya, suna kira ga shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya maido da rundunar yaki da 'yan fashi da makami da ake kira SARS, lura da dimbim matsalolin tsaron da yankinsu ke fama da su.

Talla

Wannan na zuwa ne jim kadan da shugaba Buhari ya sanar da rusa rundunar biyo bayan zanga-zangar da aka gudanar a wasu sassan kasar domin nuna bacin rai kan yadda dakarun na SARS ke cin zarafin jama'a tare da kwace dukiyoyinsu baya ga kisan jama'a a wasu lokutan.

Sai dai kungiyoyin fararen hula a jihar Borno sun ce, sam basu amince da matakin rusa wannan runduna ba lura da muhimmancinta a yaki da 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton da wakilinmu Bilyaminu Yusuf ya aiko mana daga birnin Maiduguri.

Mu dai Buhari ka dawo mana da SARS- 'Yan Borno

Daya daga cikin jagororin zanga-zangar, Kwamared Lucy Yunana ta ce, suna samun barci ne a Borno saboda tsaron da rundunar SARS ke ba su a jihar.

Yunana ta bukaci shugaba Buhari da ya kafa wani kwamiti da zai kewaya sassan Najeriya domin jin ra'ayoyin jama'a game da kawo karshen rundunar ta SARS.

Ana dai ci gaba da cece-kuce kan matakin rusa rundunar, inda wasu ke yabawa, yayin da wasu ke kokawa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.