Najeriya-Kaduna

El Rufa'i ya roki sabon sarkin Zazzau ya zama mai adalci ga al'ummarsa

Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i.
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i. RFI Hausa / Aminu Sani Sado

Gwamnatin Jihar Kaduna da ke Najeriya Malam Nasir El Rufai ya ce batun maganar takarar Sarautar Zazzau ta kare, inda ya bukaci Sarki na 19 Ahmad Nuhu Bamalli da ya yi adalci ga daukacin mutanen masarautar sa da zai jagoranta.

Talla

Gwamnan ya bayyana haka ne lokacin da ya karbi tawagar Sarkin a fadar gwamnati lokacin da su ka ziyarce shi domin nuna godiya da nadin da aka masa.

El Rufai ya ce bukatar sa ita ce Sarki Bamalli ya hada kan jama’a wajen daga darajar Masarautar Zazzau da kuma tabbatar da zaman lafiyar ta da cigaba wajen yin adalci ga kowa.

Gwamnan ya ce yanzu ba lokaci ne na duba wadanda suka goyi bayan sa ko kuma wadanda suka yi adawa da shi ba, domin kuwa lokaci ne na fara aiki wajen hada kan kowa da kowa domin samar da cigaba da kuma kare martabar Masarautar da su ke matukar ganin kimar ta.

Sabon Sarkin na 19, Amb Nuhu Bamalli ya ce sun kai ziyarar ce domin nuna godiya da zabin sa da aka yi don gadar marigayi Dr Shehu Idris a matsayin Sarkin Zazzau.

Sarkin ya ce ya san cewar zabin ba abu ne mai sauki ba ganin irin yadda aka gudanar da takara da kuma tantance masu neman Sarautar, inda ya jaddada biyayyar Masarautar ga gwamnatin jihar Kaduna.

Sabon Sarkin ya ce tawagar sa ta kunshi daukacin mutanen da suka fito daga gidajen sarautar Zazzau wanda ke nuna hadin kai da zaman lafiyar suke da shi, inda ya ke cewa bashi da hujjar ware wani bangare daga cikin Masarautar saboda dukkan su ‘yan uwan juna ne.

Sarkin Zazzau na 19 ya ce a matsayin sa na wanda ya rike Sarautar Magajin Gari na shekaru 19 yana da kwarewar da zai tafi da kowa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI