Halin Buhari na cutar da Najeriya- Dattawan Arewa
Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta bayyana damuwa kan yadda shugaban kasar Muhammadu Buhari ke nuna halin ko-in-kula kan wasu lamurra da ke wakana a kasar da suka hada da matsalar tsaro da kuma koma-bayan tattalin arziki.
Wallafawa ranar:
Kungiyar ta kuma bukaci shugaban da ya sallami shugabannin rundunonin tsaron kasar ganin yadda tura ta kai bango dangane da matsalolin tsaron da suka ki ci suka ki cinyewa musamman a yankin arewacin Najeriya.
Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da Muhammad Sani Abubakar ya yi da Dr. Hakeem Baba Ahmed, daya daga cikin jagororin Kungiyar Arewacin Najeriya.
Halin Buhari na cutar da Najeriya- Dattawan Arewa
"Abin da muke gani shi ne shugaban kasa Buhari ya yi garambawul a mulkinsa. Shi kan shi ya canza kan shi" inji Baba Ahmed.
Kungiyar ta bukaci shugaban da ya mayar da hankali kan abubuwa uku da suka hada da yaki da talauci, samar wa matasa aiki da kuma tabbatar da tsaro.
Kazalika kungiyar ta zargi shugaban da kin tilasta wa jami'an gwamnatinsa gudanar da ayyukan da suka rataya a wuyansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu