Najeriya

Makomar kujerar shugaban hukumar zaben Najeriya na cike da rudani

Shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu.
Shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu. Ventures Africa

Tababa da rashin tabbas sun mamaye makomar shugaban Hukumar Zaben Najeriya, Farfesa Mahmood Yakubu wanda wa’adin shugabancinsa zai kare ranar 9 ga watan gobe, ba tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake gabatar da sunan sa ga Majalisa ba domin ba shi damar yin wa’adi na biyu.

Talla

Rashin gabatar da sunan Farfesa Mahmood cikin jerin sunayen kwamishinonin da shugaban kasa Buhari ya gabatarwa Majalisa ranar litinin domin amincewa da nadin su ya dada sanya shakku kan sake bai wa shugaban damar cigaba da aiki a hukumar.

A wasikar da shugaban kasa ya rubutawa Majalisar Dattawa, ya bukaci amincewa da nadin Farfesa Muhammad Sani Kalla daga Jihar Katsina da Lauretta Onochie daga Jihar Delta da Farfesa Kunle Cornelius Ajayi daga Jihar Ekiti da Saidu Babura Ahmad daga Jihar Jigawa a matsayin kwamishinoni.

Wasikar ba ta ce komai kan batun shugaban hukumar Farfesa Mahmood ba, abinda ke nuna alamar cewar watakila shugaban kasa na iya sauya shi da wani.

Ya zuwa yanzu dai kallo ya koma fadar shugaban kasa domin ganin wanda za a gabatar da sunan sa domin tantancewa ganin wa’adin shugaban Hukumar na daf da karewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI