Bakonmu a Yau

Tattaunawa da Farfesa Jibrin Ibrahim kan zanga-zangar bukatar rusa sashen 'yansandan SARS

Wallafawa ranar:

A Najeriya an shiga rana ta takwas ana ci gaba da bore a wasu sassan kasar inda matasa ke neman Hukumomin kasar su aiwatar a zahiri ikirarin rusa ayarin ‘yan sandan yaki da ‘yan fashi da makami da ake kira SARS.Yayinda a wasu sassan kasar masu boren ke neman a soke rundunar ‘yan sandan, a yankunan arewa maso gabashin kasar da kuma Jihar Katsina masu boren na goyon bayan kada a ruwa ‘yan sandan domin su suke yakar ‘yan kungiyar Boko Haram.Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Farfesa Jibrin Ibrahim mai lura da lamurran kasar kuma ga bayanin da yayi.

Zanga-zangar bukatar rusa sashen rundunar 'yansanda na SARS mai yaki da fashi da makami.
Zanga-zangar bukatar rusa sashen rundunar 'yansanda na SARS mai yaki da fashi da makami. REUTERS/Temilade Adelaja
Sauran kashi-kashi