Gwamnonin Arewacin Najeriya sun ki amincewa da rusa SARS
Wallafawa ranar:
A Najeriya Gwamnonin jihohin arewacin kasar 19 sun nuna rashin amincewarsu da matakin soke sashen rundunar ‘yan sandan kasar na musamman mai yaki da ayyaukan fashi da makami da ake kira SARS.
A wata ganawa da shugaba Muhammadu Buhari, tawagar Gwamnonin bisa jagoranci Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, da ke matsayin shugaban kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriyar, ya ce sam ba mafita ba ce rushe sashen na SARS.
Acewar Lalong babu ta yadda za a ce rundunar ta SARS ta kunshi iyakar bata-gari zalla, domin kuwa cikinta akwai tarin jami’ai da ke aiki tukuru, kuma cikin amana don magance matsalolin fashin da makami da sauran muhimman kalubalen da suka addabi Najeriyar.
A jawabinsa, Gwamna Lalong ya bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya da ta sake fasalin rundunar, ta inda za ta samu damar gudanar da aikinta yadda ya kamata.
Kusan makwanni biyu al'umma Najeriyar a matakin jihohi suka shafe suna zanga-zangar bukatar rusa rundunar ta SARS wadda ta kai ga rikici tsakanin masu gangamin da jami'an tsaro a wasu sassa, kafin daga bisani gwamnatin ta amince da rusa rundunar a makon jiya.
Sai dai masana harkokin tsaro na ganin bata-gari kadai ke murna da matakin rusa rundunar ta yadda za su ci gaba da cin karensu babu babbaka.
Tuni dai Gwamnatin Najeriyar ta sanar da sabuwar rundunar SWAT a matsayin wadda za ta maye gurbin SARS don ci gaba da yakar ayyukan fashi da makami, ko da ya ke masu zanga-zangar sun ci gaba da bore kan matakin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu