Najeriya

Gwamnatin Najeriya za ta bai wa ASUU biliyan 30

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta amince ta biya Naira biliyan 30 a matsayin kudaden alawus ga malaman jami’o’in kasar.

Ministan Kwadagon Najeriya Dr Chris Ngige da ya jagoranci zaman cimma yarjejeniyar da ASUU
Ministan Kwadagon Najeriya Dr Chris Ngige da ya jagoranci zaman cimma yarjejeniyar da ASUU Daily Post
Talla

Gwamnatin za ta biya kudaden ne kashi-kashi tsakanin watan Mayu na 2021 da kuma Fabairun 2022.

Kazalika gwamnatin ta yi alkawarin ware Naira biliyan 20 domin inganta bangaren ilimi, matakin da ke zama wani bangare na cimma yarjejeniyar kawo karshen yajin aikin watanni bakwai da Kungiyar Malaman Jami’o’in ke yi yanzu haka.

Ministan Kwadagon Najeriya, Chris Ngige ya bayyana fatan cewa, Kungiyar ASUU za ta soke yajin aikinta nan kusa, yana mai cewa, gwamnati na ta kokarin lalubo hanyar kawo karshen yajin aikin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI