Najeriya

Hukumar 'Yan Sandan Najeriya za ta kori jami'anta 37

Wasu 'Yan Sandan Najeriya.
Wasu 'Yan Sandan Najeriya. The Guardian Nigeria

Yayin da ake ci gaba da zanga-zangar adawa da cin zarafin da wasu ‘yan sanda ke yi a Najeriya, hukummar lura da ayyukan ‘yan sandan kasar PSC ta sanar da shirin korar jami’an rusasshiyar rundunar SARS daga aiki.

Talla

Baya ga korar jami’an 37, ana sa ran hukumar ‘yan sandan ta hukunta wasu karin jami’an 24 bisa tuhume-tuhumen karya dokokin aiki.

Matakin dai ya biyo bayan karbar rahoton kwamitin da fadar shugaban Najeriya ta kafa tun a shekarar 2018, wanda ta dorawa alhakin yin garambawul ga sashin rundunar ‘yan sandan kasar mai yaki da fashi da makami da sauran manyan laifuka na SARS da aka rusa a baya bayan nan.

Sakataren hukumar kare hakkin dan adam ta Najeriya Tony Ojukkwu ne ya gabatar da rahoton binciken ga shugaban hukumar lura da ayyukan ‘yan sandan Najeriyar a Abuja, ranar Juma’ar da ta gabata 16 ga watan Oktoba.

An dai dade ana gabatar da korafe-korafe daban daban da suka shafi tauye hakkin dan adam kan jami’an ‘yan sandan Najeriya, wadanda a wasu lokutan wasu daga cikinsu ke halaka mutane akan hanyoyi kan kudade kalilanda suka tilasta basu, tsare mutane ba tare da hakki ba, da kuma gana musu azaba, da dai sauran nau’’o’in cin zarafin adam.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.