Najeriya-Kano

Matasa sun cigaba da zanga-zanga kan matsalar tsaro a arewacin Najeriya

Wasu matasa a Kano da ke zanga-zangar neman kawo karshen matsalolin tsaro a arewacin Najeriya
Wasu matasa a Kano da ke zanga-zangar neman kawo karshen matsalolin tsaro a arewacin Najeriya Daily Trust

Gamayyar kungiyoyin fararen hula na arewacin Najeriya sun sha alwashin ci gaba da zanga-zangar lumana yau asabar a jihar Kano, kan neman gwamnati ta dauki matakan kawo karshen matsalolin tsaro da suka addabi yankin arewacin kasar.

Talla

Kungiyoyin hadin kan arewacn Najeriyar sun sha alwashin cigaba da zanga-zangar ce duk da farmakin da wasu gungun mutane dauke da makamai suka kaiwa wasunsu, a ranar Alhamis, inda aka jikkata akalla mutane 40 ciki har da wasu manema labarai.

Jagororin masu zanga-zangar dai sun zargi gwamnati da daukar hayar gungun mutanen da suka kai musu farmakin.

Sai dai yayin ganawa da manema labarai a garin Kano shugaban gamayyar kungiyoyin fararen hular arewacin Najeriyar Balarabe Rufa’i, ya ce sun yanke kauna daga salon jagorancin manyan ‘yan siyasar arewacin kasar, sakamakon yadda suka yi nuna halin ko in kula ga bukatun magance matsalolin da suka addabi yankin.

Barabe Rufa’i ya sha alwashin cigaba da jagorantar zanga-zangar kan matsalolin tsaron a jihohin arewacin Najeriya 19 har sai sun shaida daukar matakai na gaske daga gwamnati.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.