Najeriya

Babban Sifeton 'yan sanda zai gurfana gaban majalisa saboda bata-garin rundunarsa

Wasu masu zanga-zangar bacin rai kan cin zarafin da wasu 'yan sanda ke yi a Najeriya.
Wasu masu zanga-zangar bacin rai kan cin zarafin da wasu 'yan sanda ke yi a Najeriya. Temilade Adelaja/Reuters

Majalisar wakilan Najeriya ta baiwa Babban Sifeton ‘yan sandan kasar Muhammad Adamu wa’adin mako 1 da ya bayyana gaban hadin gwiwar kwamitocinta kan Shari’a, kare hakkin dan Adam da kuma ayyukan ‘yan sanda.

Talla

Zauren majalisar wakilan ya ce, Babban Sifeton ‘yan sandan zai gurfana gaban kwamitocin nata ne kan zarge-zargen da suka dabaibaye rundunarsa na cin zarafin jama’a da kuma aikata kisan gilla.

Majalisar wakilan za ta kuma tura tawagogi zuwa shiyyoyin kasar 6 don sauraron korafe-korafen jama’a, da iyalan wadanda suka fuskanci cin zarafi da kisan gilla a hannun bata-garin jami’an ‘yan sanda, musamman na rundunar SARS masu yaki da fashi da makami da aka rusa, sakamakon zanga-zangar neman daukar matakin da matasa ke yi a sassan Najeriya.

Yanzu haka dai an shafe sama da mako guda matasa a wasu biranen Najeriyar na cigaba da zanga-zangar da suka yi wa take da #EndSARS, ta nuna bacin rai kan cin zarafin da ‘yan sanda ke yi wa jama’a, inda suke neman a yiwa daukacin rundunar jami’an garambawul.

Duk da rusa rundunar ta SARS da kuma maye gurbinta da SWAT, masu zanga-zangar sun sha alwashin cigaba da fafutuka har sai sun ga alkawuran da gwamnati da daukar musu a aikace.

Alwashin masu zanga-zangar ne kuma ya sanya ko a jiya Juma’a aka fuskanci mummunan cinkoson ababen hawa ciki da wajen a birnin Legas, sakamakon yadda suka mamaye manyan titunan jihar, gami da babbar hanyar da ta tashi daga garin na Legas zuwa Ibadan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.