Najeriya

"Cika alkawura muke bukata ba neman gafara ba"

Masu zanga-zanga a birnin Legas, dake nuna bacin rai kan cin zalin da wasu 'yan sanda ke yi a Najeriya.
Masu zanga-zanga a birnin Legas, dake nuna bacin rai kan cin zalin da wasu 'yan sanda ke yi a Najeriya. Temilade Adelaja/Reuters

Masu zanga-zangar #EndSARS ta nuna bacin rai kan cin zalin da wasu ‘yan sanda a Najeriya ke yi, sun bukaci ganin gwamnati ta dauki matakan gaggawa wajen kawo karshen matsalolin da suke kokawa akai, a maimakon afuwarsu da mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ya nema a karshen makon nan.

Talla

Farfesa Osinbajo ya gabatar da neman afuwar ce a sanarwar day a rabawa manema labarai, inda ya bayyana cewar gwamnati na daukar matakai daban daban wadanda za su taimaka wajen yin garambawul ga ayyukan ‘yan sanda da kula da rayuwarsu, horar dasu da kuma inganta ayyukansu.

Osinbajo ya yi alkawarin cewar babu wani daga cikin jami’an tsohuwar rundunar SARS da aka rusa da zai taka rawa a cikin sabuwar rundunar SWAT da aka kafa, don ganin an kakkabe hannayensu baki daya.

A cikin sakon da ya walllafa, mataimakin shugaban Najeriyar yace “Yaku ‘yan Najeriya, mun san cewar da yawa daga cikin sun harzuka, kuma mun yarda da haka. Ya dace mu dauki matakin gaggawa, saboda haka, ku yafe mu”

Sai dai a martaninsu, masu zanga-zangar ta #EndSARS, sun ce ba za su karbi bukatar neman afuwarsu ba, har sai gwamnati ta cika dukkanin alwauran da ta dauka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.