Najeriya

Matasa sun yi addu’o’in neman mafita daga matsalolin da Najeriya ke ciki

Wasu 'yan Najeriya yayin zanga-zanga kan neman yiwa rundunar 'yan sandan kasar garambawul.
Wasu 'yan Najeriya yayin zanga-zanga kan neman yiwa rundunar 'yan sandan kasar garambawul. Reuters

Yayin da ake cigaba da zanga-zangar bacin rai kan cin zalin da wasu ‘yan sanda ke yi a Najeriya da ya kai ga rusa rundunar SARS, matasa sun gudanar addu’o’in neman kawo karshen matsalolin da kasar ke ciki, yayin cigaba da yin tattakin.

Talla

Rahotanni sun ce daga cikin garuruwan da tattakin gami da addu’o’in ga kasa suka gudana akwai Minna dake jihar Niger mai fama da hare-haren ‘yan bindiga, sai Kano, Rivers, Delta, Imo, Ogun, da kuma jihar Legas.

Tuni dai rundunar ‘yan sandan Najeriya ta rusa bangarenta mai yakar manyan laifuka na SARS day a zama silar fara wannan zanga-zanga, inda tam aye gurbin rundunar ta musamman da SWAT da a yanzu ake cigaba da shirye-shiryen kafuwarta.

Masu zanga-zangar ta #EndSARS dai sun sha alwashin cigaba da fita kan tituna har sai sun shaida cika alkawuran da gwamnatin Najeriya ta daukar musu ciki kuwa harda yiwa daukacin rundunar ‘yan sandan kasar garambawul.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.