Najeriya

EndSARS:Akwai masu son a raba Najeriya-Gwamnan Yobe

A yayin da aka shiga rana ta 12 da soma gudanar da zanga-zangar #EndSARS domin nuna bacin rai kan yadda jami'an 'yan sanda ke cin zalin mutane a Najeriya, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya bayyana cewa, akwai wasu mutane da ke son a raba kasar tare da jefa ta cikin rudani. 

Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni
Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni theinterview
Talla

Gwamnan ya ce, a yayin da wasu ke hankoron ganin an shafe rundunar SARS baki daya, wasu kuwa musamman 'yan arewacin Najeriya na bukatar dakarun saboda muhimmancinsu wajen yaki da matsalolin tsaro da suka hada da rikicin Boko Haram da satar jama'a da kuma hare-haren 'yan bindiga.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hirar da gwamnan ya yi da manema labarai a karshen mako.

EndSars:Akwai masu son a raba Najeriya-Gwamnan Yobe

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI