Najeriya-Lagos

Gwamnatin Lagos ta kulle ilahirin makarantu saboda tsanantar zanga-zanga

Matakin kulle makarantun na zuwa kwanaki kalilan bayan dawowa daga dogon hutun da coronavirus ta tilasta tafiya na kusan watanni 7.
Matakin kulle makarantun na zuwa kwanaki kalilan bayan dawowa daga dogon hutun da coronavirus ta tilasta tafiya na kusan watanni 7. Thomson Reuters Foundation/Kieran Guilbert

Gwamnatin Jihar Lagos a kudancin Najeriya ta sanar da kulle ilahirin makarantun jihar kwanaki kalilan bayan budesu, saboda tsanantar zanga-zangar masu neman rusa SARS da ke kokarin juyewa zuwa rikici a sassan kasar.

Talla

Sanarwar da kwamishinar ilimin jihar Folasade Adefisanyo ta fitar da sa hannun kakakinta Kayode Abayomi ta bukaci kulle makarantun saboda tsaron lafiyar dalibai da malamai wadda ta ce suna cikin barazana a halin da ake ciki.

Matakin Gwamnatin na Lagos na zuwa kwana guda bayan bude sauran makarantun da basu riga sun bude ba mako guda da ya gabata ba bayan dogon hutun da coronavirus ta tilasta tafiya, ciki har da rukunin makarantun rainon kananan yara da suka kunshi daycare da Kindergarten.

A jawabin kwamishinar cikin sanarwar wadda aka rarrabawa manema labarai, ta shawarci iyaye da su sanya idanu kan yaransu don ganin basu shiga zanga-zangar ba, wadda ke ci gaba da tsananta.

Zuwa yau Talata dai galibin ma’aikata a jihar ta Lagos basu da hanyoyin wucewa zuwa wuraren aiki bayanda masu zanga-zangar suka rufe duk wasu manyan titunan sufuri, a bangare guda kuma su ke ci gaba da bannata kayakin jama’a baya ga farmakar jami’an tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.