Najeriya-Zanga zanga

Kungiyar Dattawan Arewa na fargabar shigar bata-gari cikin masu zanga-zanga

Wasu masu zanga-zanga a Lagos.
Wasu masu zanga-zanga a Lagos. Temilade Adelaja/Reuters

Kungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta bukaci kawo karshen zanga-zangar bukatar rusa sashen rundunar ‘yansanda na musamman da ake yiwa lakabi da SARS mai yaki da ayyukan Fashi da Makami wadda aka shafe kusan makwanni 2 ana yi a sassan kasar galibi kudanci.

Talla

Sanarwar da kungiyar ta fitar daren jiya litinin dauke da sa hannun sakataren yada labaranta Hakim Baba-Ahmed ta bayyana nasarar da masu zanga-zangar suka samu ta kawo karshen rundunar SARS wadda ake zargi ta tafka kura-kurai a matsayin babban ci gaba, sai dai ta ce ci gaba da gangamin zai shafi walwala jama’ar da basu ji ba basu gani ba.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, akwai fargabar ci gaban zanga-zangar ya janyo bata-gari cikinta da ke da manufa ta daban sabanin wadda aka faro zanga-zangar dominta.

Jaridar PREMIUM TIMES a Najeriyar ta ruwaito cewa jami’an ‘yansandan kasar sun yi hayar ‘yan daba da ‘yan sara-suka don tarwatsa dandazon masu zanga-zangar a sassa daban-daban.

Zuwa yanzu dai zanga-zangar wadda ta faro daga shafukan sada zumunta gabanin bazuwar jama’a a biranen kasar ta lakume rayukan mutane 15 a cewar kungiyar Amnesty International.

Bukatar ta kungiyar dattawan Arewacin Najeriyar ta zo dai dai da kiran Sarkin Ife Adeyeye Ogunwusi tare da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo da suka bukaci tsagaitawa da zanga-zangar wadda ke neman juyewa rikici tsakanin jami’an tsaro da fararen hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.