#EndSars

Babu wanda ya rasa rayuwarsa a harbin masu zanga-zanga - Sanwo - Olu

Gwamnan Legas Baba Jide Sanwo-Olu lokacin da ya ziyarci asibi domin ganin wadanda suka ji rauni bayan harbi jami'an tsaro kan masu zanga-zanga a harabar Lekki
Gwamnan Legas Baba Jide Sanwo-Olu lokacin da ya ziyarci asibi domin ganin wadanda suka ji rauni bayan harbi jami'an tsaro kan masu zanga-zanga a harabar Lekki Sanwo-Olu

Gwamnan Jihar Lagos dake Najeriya Babajide Sanwo Olu yace babu wanda yam utu a hanyar Lekki lokacin da jami’an tsaro suka yi harbi wajen taron masu zanga zangar adawa da zargin cin zarafin Yan Sanda, sai dai mutane akalla 25 sun samu raunuka daban daban.

Talla

A jawabin da ya yiwa jama’ar jihar kan halin da ake ciki, Sanwo Olu yace sun dan samu natsuwar cewar babu wanda ya rasa ran sa a wurin kamar yadda ake ta yayatawa ta kafar sada zumunta.

Gwamnan yace ya bada umurnin gudanar da bincike kan matakin da sojoji suka dauka lokacin da aka kai su hanyar Lekki daren jiya, yayin da ya bayyana dakatar da ayyukan gwamnati na kwanaki 3 domin mayar da hankali kan harkokin da suka shafi tsaro.

Sanwo Olu ya shaidawa masu zanga zangar cewar yana tare da su kuma yana jin irin radadin da suke ji sakamakon abinda ya faru daren jiya, inda ya buka ce su da su kwantar da hankalin su.

Kungiyar Amnesty International ta bayyana cewar an kasha mutane da dama a harbin da ake zargin jami’an sojin da yi a hanyar Lekki, zargin da rundunar sojin ta bayyana a matsayin labaran karya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.