#EndSars

Buhari ya bukaci jama’a da su kwantar da hankula dangane da batun EndSars

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari yayin taron kwamitin gudanarwar kasa
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari yayin taron kwamitin gudanarwar kasa © Nigeria Presidency

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci jama’ar kasar da su kwantar da hankalin su bayan guda bayan an zargin jami’an tsaron kasar da harbin masu zanga zanga a birnin Lagos.

Talla

Sanarwar da fadar shugaban kasar ta rabawa manema labarai tace shugaban kasar a shirye yake ya aiwatar da sauye sauyen da ake bukata a rundunar Yan Sandan kasar.

Sanarwar da Femi Adeshina ya rabawa manema labarai tace Buhari ya bukaci daukacin jama’ar kasar da su kwantar da hankalin su yayin da matakan da gwamnatin jihohi suka dauka na kafa kwamitin shari’a domin gabatar da korafe korafen da ake da su kan jami’an tsohuwar rundunar SARS da aka rusa, inda ya sha alwashin taimaka musu wajen ganin sun tabbatar da adalci a ayyukan su.

Sanarwar tace soke rundunar SARS da shugaba Buhari ya bada umurni alama ce dake nuna cewar gwamnatin a shirye take ta sauya fasalin ayyukan Yan Sandan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.