#EndSars

Masu zanga-zangar EndSars sun kona cibiyar Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya

Rikicin da ya biyo bayan zanga zangar adawa da cin zarafin da ake zargin 'Yan Sanda da shi a Najeriya na cigaba da haifar da matsaloli a Lagos ganin yadda yanzu haka aka cinnawa Hukumar dake kula da tashoshin jiragen ruwan Najeriya dake anguwar Marina na jihar wuta.

An kona cibiyar Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya NPA dake Legas
An kona cibiyar Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya NPA dake Legas Daily Trust
Talla

 Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewar majiyoyi sun shaida mata cewar wasu mutane dake fushi da yadda gwamnati ta kai sojoji wajen tarwatsa masu zanga - zanga a hanyar Lekki ne suka cinnawa ginin wuta.

Yanzu haka jami’an kwana-kwana na can suna kokarin kashe gobarar da ta tashi a wutar.

Rohatanni sun tabbatar da cewa, tun bayan tura sojoji cibiyar masu zanga-zangar dake Lekki Tallgate, lamarin ya kara rincabewa, inda fusatattu suka fara kone-kone tun a daren na Talata ciki harda shingen karban harajin ababen hawa na Lekki Tallgate da wasu manyan Otel da asibiti.

Yayin da Laraban nan kuma masu zanga-zangar suka ci gaba da kone-konen, inda rahotanni suka ce, wasu da ake zargin 'yan daba ne sun kai hari gidan talabijin na TVC da ke Legas din.

Wata ma'aikaciyar gidan talabijin din ta wallafa a shafinta na Twitter cewa suna cikin gabatar da shiri kai tsaye dole suka katse sakamakon 'yan daban da suka tinkaresu yayin gabatar da shirye-shiye.

Rahotanni na nuna cewa gidan talabijin din mallakar tsohon gwamnan Legas kuma jagoran APC Bola Ahmed Tinubu ne. 

Kazalika, masu zanga-zangar sun bankada wuta a tashar motocin BRT na gwamnatin Lagas dake Oyingbo, inda motoci da dama suka kone.

A bangare daya, bayanai da wasu hoton bidiyo dake yawo a kafafen sada zumunta sunce, fusatattun masu zanga-zangar sun kona gidansu gwamna Baba Jide Sanwo - Olu, inda yanzu haka mahaifiyarsa ke rayuwa a ciki.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI