#EndSars

Soyinka ya zargi gwamnatin Najeriya da kamakarya kan EndSars

Fitaccen Marubucin Najeriya Wole Soyinka
Fitaccen Marubucin Najeriya Wole Soyinka PIUS UTOMI EKPEI / AFP

Fitaccen Marubucin Najeriya Farfesa Wole Soyinka ya yi Allah wadai da yadda sojoji suka yi amfani da karfi wajen tarwatsa masu zanga zangar lumana domin adawa da zargin cin zarafin jama’a da ake yiwa tsohuwar rundunar SARS.

Talla

Sanarwar da ya rabawa manema labarai na kunshe da zargin gwamnatin tarayya da yin gaban kan ta wajen tura sojoji masu dauke da makamai kan masu zanga zangar.

Soyinka yace ya zama wajibi a shaidawa wannan gwamnatin cewar sojoji sun maye gurbin SARS domin murkushe masu zanga zanga, domin kuwa binciken say a tabbatar masa cewar ba Gwamnan Lagos ya bukaci tura sojojin ba, kuma bai yi korafi kan tabarbarewar tsaro ba.

Marubuchin yace gwamnatin tarayya tayi amfani da kama karya wajen haifar da rauni mai zurfi a tunanin jama’a.

Soyinka yace lokacin da ya isa Abeokuta mahaifar sa ya gamu da wurin binciken ababan hawa amma bai fuskanci matsala ba, kuma ya san cewar ana cigaba da sanya irin su a daidai lokacin da yake rubuta wannan sanarwa.

Fitaccen marubucin yace abin takaici ne da kuma rashin hankali wasu mutane su dinga fadin cewar zanga zangar na illa ga tattalin arzikin kasa da kuma sauran su.

Marubuchin yace annobar korona tayi matukar illa ga tattalin arzikin Najeriya na sama da watanni 8 kuma da wuya a mayar da asarar da akayi, amma kuma rayukan ‘yan Najeriya sun zama mafi sauki da za’a yiwa hawan kawara har ma da bada lambar girma kamar yadda shaidu suka nuna wajen jika tutar Najeriya da jinin daya daga cikin wadanda aka kashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI