#EndSars

Buhari ya shaidawa tsoffin shugabannin Najeriya yadda zanga-zangar EndSars ta zama tarzoma

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari yayin jagorantar taron majalisar kasa
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari yayin jagorantar taron majalisar kasa © Nigeria Presidency

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaidawa taron Majalisar koli da ta kunshi tsoffin shugabannin kasar cewar duk da amincewa da bukatun matasa masu bukatar sauyi kan rundunar SARS zanga zangar ta rikide ta zama tarzoma wadda ta kaiga rasa rayuka da asarar dukiyoyi.

Talla

Sanarwar da mai bashi shawara kan harkokin yada labarai Femi Adeshina ya rabawa manema labarai tace shugaban ya shaidawa tsoffin shugabannin irin bukatun matasan da ya amince da su ciki harda rusa rundunar SARS da kuma fara aiwatar da sauye sauye ga rundunar Yan Sanda.

Buhari yace abin bakin ciki shine yadda masu zanga zangar suka ki janye ta wajen tatatunawa da gwamnati domin ganin yadda za’a kawo sauyin, har at kaiga komawa tarzoma.

Shugaban ya bayyana damuwa kan yadda tarzomar ta haifar da rasa rayuka da lalata kadarorin gwamnati da na jama’a, yayin da yayi alkawarin cigaba da gabatar da jagoranci na gari.

Sanarwar tace tsoffin shugabannin duk sun yabawa Buhari kan matakan da ya dauka na dawo da doka da oda wajen jawabin da ya yiwa al’ummar kasar da kuma kwantar da hankalin jama’a.

Tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya yabawa Buhari kan jawabin da yayi daren jiya wanda yace al’ummar kasar sun dade suna jira, da kuam amincewa da bukatun matasan da shugaban kasar yace yana aiki akai.

Tsoffin shugabannin sun mika sakon ta’aziyyar su ga mutanen da suak rasa ‘yan uwan su cikin su harad fararen hula da sojoji da kuma yan sanda, yayin da suka jadadda matsayin sun a tabbatar da doka da oda da kuma ‘yancin yan kasa, ciki harad zanga zangar lumana.

Tsoffin shugabannin sun yi Allah wadai da yunkurin raba kan jama’a ta hanyar ‘yan aware inda suka bukaci dakatar da haka, yayin da suka yabawa matakan da gwamnonin jihohi suka dauka na kafa kwamitin bincike domin bincike kan zarge zargen da ake yiwa jami’an yan sandan.

Da karshe tsoffin shugabannin sun bukaci matasa da su nemi bukatun su ta hanyar tattaunawa da gwamnati, yayin da ita ma gwamnatin aka bukace ta da ta gudanar da taro da su da masu ruwa da tsaki a cikin kasar.

Cikin wadanda suka halarci taron sun kunshi daukacin tsoffin shugabannin dake da rai da suka hada da Janar Yakubu Gowon da Olusegun Obasanjo da Janar Ibrahim Babangida da Chief Ernest Shonekan da Janar Abdusalami Abubakar da Dr Goodluck Jonathan da kuma mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da hafsoshin sojin kasar da kuma wasu ministoci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.