Legas ta yi asarar sama da naira biliyan 400 a zanga-zangar #EndSars
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:28
Rohatanni daga jihar Legas a Najeriya na cewa gwamnatin jihar ta yi asarar kimanin Naira miliyan 400 sakamakon rikicin da ya barke a jihar, biyo bayan zanga-zangar EndSars da ake yi, duk da cewa har yanzu ba'a kammala bincika ba, yayin da Juma’an nan gwamnan Jihar Babajide Sanwo-Olu ya aki rangadin gani da ido na wuraren da aka yi ta'adi sakamakon tarzomar.
Shugaban Cibiyar Kasuwanci Ta Legas, Muda Yusuf, ya shaidawa manema Labarai, cewa har yanzu ba'a kai ga tattara alkaluma kan kiyasin asarar da wannan tarzoma ta jawo ba, amma an yi asarar kimanin naira biliyan 400.
Tarzomar da ta barke a Legas ta haifar da matsaloli da ta kai ga kona gine-ginen gwamnati da na al’umma.
Cikin wuraren da aka kona tun a daren Talata kafin wayewar Laraba, sun hada da wani Babban Otel da wani asibiti baya ga ofisoshin ‘yan sanda.
Yayin da ranar Laraba aka cinna wuta a cibiyar Hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya NPA, da kuma gidan talabijin na TVC da ke Legas din, tare da ofishin Hukumar kiyaye haddura da wani sashe na sakatariyar Legas.
Kazalika, fusatattun masu zanga-zangar sun bankawa tashar motocin BRT na gwamnatin Lagas dake Oyingbo wuta, inda motocin Bus na safa-safa da dama suka kone, yayin da aka kai hari kan bankuna a wasu sassan birnin.
A bangare daya, bayanai sunce ankuma kona gidan mahaifiyar gwamnan jihar Baba Jide Sanwo – Olu, yayin da suka farma gidan sarkin Lagas, wanda yasha da kyar, inda aka wawure kayayyakinsa da dukiyoyi.
Dangane da wannan batu, Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Dr. Kasimu Garba Kurfi masanin tattalin arziki a Najeriya don jin yadda suke kallon irin hasarar da aka tafka.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu