#EndSars

Dan wasan Najeriya Ogu ya bukaci kauracewa wasanni saboda zanga-zangar EndSars

Dan wasan Najeriya John Ogu da ya bukaci a kauracewa wasa saboda zanga-zangar EndSars
Dan wasan Najeriya John Ogu da ya bukaci a kauracewa wasa saboda zanga-zangar EndSars Reuters

Dan wasan tsakiya na tawagar Super Eagles ta Najeriya John Ogu, ya bukaci kungiyar da ta kauracewa wasannin da ke tafe, saboda abin da ya kira matakin gwamnatin Najeriya kan masu zanga-zangar EndSars.

Talla

Dan wasan wanda ya bugawa kungiyar wasa har sau 26, yace matakin kauracewar zai kasance babban sako ga gwamnati.

Bayaga hira da ‘yan jaridu, Ogu ya wallafa a shafinsa na twitter cewa, ‘yan siyasar Najeriya su tura ‘ya’yansu zuwa filin wasa domin wakiltar Najeriya a wasanin da dama dake tafe, ciki harda na neman gurbi a gasar neman cin kofin duniya.

A ranar Talata da ta gabata shima Odion Ighalo ya ce kasar ta zama abin kunya a kasashen duniya, kan abin da ya kira harbi da jami’an tsaro sukayiwa masu zanga-zanga a Lekki Tallgate dake Lagos.

Jami'an tsaron Najeriya dai sun musanta bude wuta kan masu zanga-zangar kamar yadda akayi ta yadawa sunyi tare da hallaka fararen hula, yayin da shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci da su koma gidajensu domin tattaunawa da gwamnati kan bukatunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.