Najeriya

Najeriya: Matasa na kwasar 'ganima' a gidajen fitattun 'yan siyasa da runbunan abinci

Wasu matasa da suka fusata a Najeriya.
Wasu matasa da suka fusata a Najeriya. Dailytimes

Matasa a Najeriya na ci gaba da kai hare hare dakunan aje kayan abinci da kuma gidajen wasu fitattun 'yan siayasar kasar, inda suke kwashe kadarorin dake ciki.

Talla

Wakilinmu a Calabar ya tabbatar mana da fasa gidan mahaifin Sanata Victor Egba Ndoma inda aka kwashe daukacin kayayyakin dake ciki da kuma cinawa gidan mai mallakar gwamna Ben Ayade wuta.

Haka ma rahotanni daga Ibadan suka ce matasan sun kai hari gidan Sanata Teslim Folarin inda suka kwashe kadarori na tarin dukiya.

Rahotanni sun ce matasan dauke da adduna sun kai hari ofishin tsohon mataimakin shugaban Majalisar wakilai Lasun Yusuf inda suka yi awon gaba da Babura da wasu kayayyaki.

A jihar Plateau, Gwamna Simon Lalong ya sake dawo da dokar hana fita ta sa’oi 24 bayan daruruwan mutane sun fasa gidan da aka aje abincin tallafi inda suka kwashe baki daya.

A jihar Osun ma gwamnatin Jihar ta sake dawo da dokar hana fitar ta sa’oi 24 nigeriadomin kawo karshen hare haren da ake samu

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.