#EndSars

Buhari ya bukaci adalci ga wadanda rikicin EndSars ya shafa

Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya nuna damuwa kan kashe kashe da aka samu a kasar
Shugaban Najeriya Mohammadu Buhari ya nuna damuwa kan kashe kashe da aka samu a kasar © Nigeria Presidency

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake bukatar samun zaman lafiya a cikin kasar bayan kwashe kwanaki ana samu tarzoma da kuma sace dukiyoyin jama’a a sassan kasar.

Talla

Kalaman shugaba Buhari na zuwa ne, bayan da ya yi ta shan suka a ciki da wajen Najeriya, kan rashin cewa uffan, dangane da batun harbin masu zangar-zangar EndSars a hanyar Lekki na birnin Lagos, a lokacin da yayiwa 'yan kasar jawabi ranar Alhamis.

To sai dai shugaba Muhammadu Buhari, ta bakin Kakakinsa, Malam Garba Shehu, yace, ya guji tsokaci kan batun ne, har sai kwamitin binciken da gwamnatin jihar Legas ta kafa, ta kammala tattara bayanai akai, yana mai bayana goyan bayansa ga kwamitin, tare da ganin an tabbatar da adalci ga masu zanga-zanga da jami’an  tsaro da suka rasa rayukansu da kuma mutanen aka barnatawa dukiyoyi.

To sai dai kuma shugaban ya yi kakkausar suka da Allah wadai kan matakin wasu bata gari na satan abincin da wasu kayayyaki na gwamnati da na al’umma a wasu jihohin kasar.

Akalla mutane 11 aka tabbatar da mutuwar su a sassan Najeriyar sakamakon tirmitsitsin kwasar abincin da aka jibge a dakuna aje kayayayki na gwamnati a Jihohin Edo da Taraba da kuma Anambra, abinda ya sa gwamnatocin wasu jihohi kafa dokar hana fita na sa’oi 24.

Rahotanni sun ce bayan Lagos da Osun da aka fara samun matsalar, an kuma samu a Jihohin Edo da Anambra da Kaduna da Plateau da Cross Rivers da kuma Ekiti da kuma Adamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.