Najeriya

An kame kusan Mutane 500 da suka fasa rumbunan abinci a sassan Najeriya

Wasu 'yan Najeriya bayan wawure dakin ajiye abinci da ke birnin Jos a jihar Plateau.
Wasu 'yan Najeriya bayan wawure dakin ajiye abinci da ke birnin Jos a jihar Plateau. AFP

A Najeriya jihohi da dama sun sanya dokar hana zirga zirga ta tsawon sa’o’i 24 sakamakon yadda al’ummominsu suka shiga fasa rumbunan ajiyar kayan abinci da shaguna suna dibar kayayyaki, wanda ya kai ga kame mutane da dama da suka jagoranci aika-aikar.

Talla

Rahotanni daga sassan Najeriya na nuni da yadda dimbim al’umma a wasu jihohin Najeriya suka yi fitar dango suna farfasa duk inda su ke tsammanin an boye kayayyakin abinci da na masarufi suna awon gaba da su, kuma sun shafe ilahirin karshen makon da ya gabata suna cin karensu babu babbaka.

Wadannan mutane dai sun hada ne da mata da maza, matasa dama magidanta, wasu ma rike da ‘ya'yansu, wadanda suka yi amannar cewa kayyakin abincin da aka bayar a raba musu ne aka boye, kuma suke rage wa hukumomi aiki wajen dibar abin da suka kira nasu.

Rahotanni sun ce bayan Lagos da Osun da aka fara samun matsalar, an kuma samu a Jihohin Edo da Anambra da Kaduna da Plateau da Cross Rivers da Ekiti, baya ga Adamawa da Abuja babban birnin Najeriyar.

Tuni rundunar ‘yan sandan Najeriya ta umurci jami’anta da su shiga farautar masu fakewa da zanga zangar EndSARS suna fasa rumbunan ajiyar gwamnati da na daidaikun mutane.

Ya zuwa yanzu rahotanni sun ce kusan mutane dari 5 da ake zargi sun aikata wannan aika aika ne suka shiga komar ‘yan sanda a jihohin Lagos, Akwa Ibom, Osun, Anambra, Kano da Filato.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI