Najeriya

Rahoto kan yadda labaran karya ke tasiri wajen haddasa yamutsi a Najeriya

Wani yanki na jihar Lagos a Najeriya bayan lafawar rikicin da ya biyo bayan zanga-zangar ENDSARS.
Wani yanki na jihar Lagos a Najeriya bayan lafawar rikicin da ya biyo bayan zanga-zangar ENDSARS. REUTERS/Afolabi Sotunde

A Najeriya, al’umma na ci gaba da tafka muhawara kan tasirin kafofin sadarwar zamani ta fuskokin samar da zaman lafiya ko akasin haka, ganin yadda wasu ke amfani da kafafen wajen yada labarai marasa tushe da kalaman tunzurawa.Tasirin kafofin sadarwar zamanin dai ya sake daukar hankula ne la’akari da irin rawar da suka taka yayin zanga-zangar EndSARS wadda daga bisani ta rikide zuwa rikici. Nura Ado Suleiman ya yi duba kan wannan batu ga kuma rahoton da ya hada mana.

Talla

Rahoto kan yadda labaran karya ke tasiri wajen haddasa yamutsi a Najeriya

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.