#EndSars

Gwamnatin Legas ta tura mu Lekki - Sojin Najeriya

Babban Hafsan rundunar sojin Najeriya Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai.
Babban Hafsan rundunar sojin Najeriya Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai. Pulse.ng

Runduna ta 81 ta sojin Najeriya da ke Lagos, ta ce Gwamnatin Jihar Lagos ta gayyace ta girke sojoji bayan kafa dokar hana fita sakamakon barkewar tarzomar da ta biyo bayan zanga zangar adawa da cin zarafin 'yan Sanda.

Talla

Sanarwar da rundunar ta bayar mai dauke da sanya hannu Manjo Osoba Olaniyi tayi watsi da matsayin gwamnatin jihar Lagos cewar bata san wadanda suka gayyaci sojin ba, yayin da ta kuma musanta zargin kisan kiyashin da ake mata.

Manjo Olaniyi ya bayyana cewar zargin cewar sojojin sun aikata kisan kiyashi yarfe ne da kuma neman bata musu suna, domin babu lokacin da dakarun su suka bude wuta kan fararen hula masu zanga zanga.

Kakakin sojin yace bayan sanya dokar hana fita, gwamnatin jihar Lagos ta gayyaci sojoji domin tabbatar da ganin jama’a na mutunta ta, sakamakon kone konen da akayi na kadarori da kuma dukiya tare da kashe jami’an Yan Sanda, kuma abinda ya sa sojojin suka amsa kira kenan.

Manjo Olaniyi yace an bi duk matakan doka wajen sanya hannun sojin domin kwantar da tarzomar da aka samu kuma dakarun sun yi aikin su kamar yadda doka ta tanada.

Daga karshe sanarwar tace babu koda mutum guda da sojojin suka harbe kuma akwai shaidun dake tabbatar da haka, saboda haka duk wani zargi da ake yiwa sojin yunkuri ne na bata musu suna, saboda haka suna bukatar jama’a suyi wasti da haka.

Gwamnan Jihar Lagos Babajide Sanwo Olu ya nesanta kan sa daga gayyatar sojin inda yake cewa bai san wanda ya bada umurnin gayyatar su ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI