'Yan bindiga a Nasarawa sun sace mutane 17 a wani masallaci

Hoto dake dauke da alamar 'yan bindiga
Hoto dake dauke da alamar 'yan bindiga The Guardian Nigeria

A Najeriya wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu satar mutane ne sun garkuwa da su domin karban kudin fansa ne sun sace mutane 17, bayan da suka mamaye wani masallaci a garin Gwargwada-Sabo da ke yankin Gadabuke na jihar Nasarawa.

Talla

Jaridar Daily Trust ta gano cewa daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su har da wasu ma’aikatan dakin adana dakardu na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, cikin mata uku da maza 13 da akayi awon gaba da su.

Wani mazaunin yankin, mai suna Usman, ya ce lamarin ya faru ne a daren Talata lokacin da Musulmai ke gudanar da sallar Isha’i.

Yana mai cewa ‘Yan bindigar sunyi ta harbe-harbe ta bangarori daban-daban, a dai-dai lokacin da wasun su suka kewaye masallacin, inda sukayi awon gaba da mutanen 17 cikin daji.

Usman yace, maharan sun ware limamin masallacin garin da kananan yara a gefe guda, kafin awon gaba da mutanen.

Jaridar tace, Iyalan mazauna garin sun samu tattaunawa da ‘yan bindigar da suka bukaci naira miliyan daya kan kowane mutun a matsayin kudin fansa, bayan da a ranar farko suka bukaci miliyan 50 kan kowane mutun guda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.