Maiduguri

Zulum ya baiwa daukacin 'ya'yan Civillian JTF da aka kashe tallafin karatu

Gwamnan Barno Babagana Umara Zulum yayin bukin taimawa kungiyar sakai dake yaki da Boko Haram
Gwamnan Barno Babagana Umara Zulum yayin bukin taimawa kungiyar sakai dake yaki da Boko Haram RFI Hausa\Ahmed Abba

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bata da tallafin karatun gwamnati ga yara, akasarinsu marayu, wadanda iyayensu suka sadaukar da rayuwansu cikin kungiyar sa kai ta Civillian JTF, da suka hada da mafarauta da‘ yan banga da aka kashe a fagen daga yayin yaki da mayakan Boko Haram a cikin shekaru bakwai da suka gabata, wato tun daga shekarar 2013.

Talla

Baya daukar nauyin wadanda yara wato Scholarship a turance, gwamna Zulum ya kuma bada da tallafin jin kai na Naira miliyan 180, ga matan da aka kashe mazajen su a fagen daga, yayin taimawa sojoji, inda kowace guda ta samu naira dubu 50, tare da rarraba buhunan kayan abinci dubu 27 ga ‘yan kato da gora kimanin dubu 9.

A yayin wani buki da aka gudanar gaban mayakan na sakai kimanin dubu 9, a harabar jami’ar Maiduguri a wannan Laraba, Gwamnan ya sanar da daukan wannan matakai da bada tallafi.

Ko wane dayan mayakan na sakai dake taimawa sojojin Najeriya yaki da Boko Haram a Borno ya samu tsabar kudi naira dubu 20, da buhun shinkafa mai nauyin kilogiram 50, da katan din spaghetti da kuma galan din man girki, baya ga alawus din da suke samu na wata-wata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.