Bakonmu a Yau
Tattaunawa da Malam Iro Danfulani mazaunin yankin da aka sace Masallata 17 a jihar Nasarawar Najeriya
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:05
Yanzu haka 'yan bindiga a Jihar Nasarawa da ke Najeriya sun yi garkuwa da wasu mutane 17 da suka kama a cikin wani Masallachi da ke kauyen Kwambe a kusa da Gadabuke lokacin da suke Sallar Isha.'Yan bindigar na neman biyansu diyyar naira miliyan 17 diyya kafin sakin mutanen wadanda suka kwashe kwanaki 9 a hannun su.Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da wani mazaunin yankin Malam Iro Danfulani, kuma ga yadda zantawar su ta gudana.