#EndSars

Rundunar 'Yan sanda Najeriya tace an kashe jami'an ta 22

Sufeto janar na 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu
Sufeto janar na 'yan sandan Najeriya Mohammed Adamu Vanguard.ng

Rundunar 'Yan Sandan Najeriya tace an kashe mata jami’ai 22 a tarzomar da ta biyo bayan zanga zangar adawa da cin zarafin da ake zargin rundunar SARS dake yaki da ‘Yan fashi da makami da aka rusa a cikin wannan wata, yayin da tayi watsi da zargin cewar jami’an ta sun harbi masu zanga zanga.

Talla

Sufeto Janar na Yan Sandan kasar Muhammadu Adamu ya bayyana haka, inda yake cewa bayan wadanda aka kashe lokacin tarzomar an kuma raunata wasu da dama, yayin da aka kona ofisoshi 205.

Zanga zangar adawa da rundunar SARS ya barke ne daga ranar 8 ga wannan wata, wanda ta rike ta zama tarzoma a jihohi daban daban, abinda ya kaiga kai hare hare gine ginen gwamnati da na jama’a da rumbunan abinci da kuma shagunan kamfanoni da mutane.

Kungiyar Amnesty International ta zargi Yan Sandan da kasha mutane 12 suka mulokacin zanga zangar, a rahotan da tace an kashe fararen hula 56, amma rundunar Yan Sandan tayi watsi da zargin inda tace jami’an ta sun yi aiki kamar yadda doka ta tanada abinda ya kaiga wasu sun rasa rayukan su.

Sanarwar da kakakin Yan Sandan na kasa Frank Mba ya rabawa manema labarai tace masu zanga zangar ne suka yiwa jami’an su kisan gilla, yayin da aka raunata wasu da dama daga cikin su.

Yan sandan sun bayyana rahotan amnesty a matsayin karya da kuma yaudara.

Ita ma rundunar sojin Najeriya ta hannun kakakin ta Manjo Osoba Olaniyi tayi watsi da zargin cewar jami’an ta sun bude wuta a hanyar Lekki wajen tarwatsa masu zanga zanga, yayin da sojojin suka ce Gwamnan Lagos Babajide Sanwo Olu ya gayyace su domin tabbatar da aiki da dokar hana fitar dare, sabanin ikrarin sa cewar bai san wanda ya gayyaci sojojin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.