Najeriya-Coronavirus

Ma'aikatar Lafiyar Najeriya ta bayyana fargabar sake dawowar Coronavirus

Guda cikin cibiyoyin kula da masu Coronavirus a Jihar Kano ta arewacin Najeriya.
Guda cikin cibiyoyin kula da masu Coronavirus a Jihar Kano ta arewacin Najeriya. RFI Hausa / Abubakar Dangambo

Ministan Lafiyar Najeriya Dr Osagie Ehanire ya ce sake dawowar cutar korona Najeriya za ta yi matukar illa muddin al’ummar kasar suka cigaba da bijire ma ka’idodin da aka gindaya domin dakile ta.

Talla

Yayin da ya ke jawabi wajen taron shugabannin kungiyar kula da ma’aikatan lafiya, ministan ya ce abinda ke faruwa a nahiyar Turai da Amurka ya dace ya zama darasi ga 'yan Najeriya ganin yadda dimbin jama’ar kasar ke tafiye tafiye zuwa kasashen.

Ehanire ya bukaci yan kasuwa da gwamnatocin jihohi da su tashi tsaye wajen fahimtar da jama’a bin ka’idodin da aka gabatar domin kare kan su daga kamuwa da cutar musamman wajen wanke hannu da sanya kyallen dake rufe fuska da kuma nesanta kai daga taruwar jama’a da yawa.

Hukumar yaki da cutar ta sanar da samun karin mutane 170 da suka harbu da cutar, yayin da mutane 3 suka mutu, abinda ya kawo adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya zuwa dubu 62 da 853, kuma daga cikin su 1,114 sun mutu, kana 58,675 sun warke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.