Najeriya

Najeriya:'Yan bindiga sun sace mutane a wani asibiti

'Yan bindiga masu satar mutane sai cin karensu suke ba babbaka a arewacin Najeriya.
'Yan bindiga masu satar mutane sai cin karensu suke ba babbaka a arewacin Najeriya. The Guardian Nigeria

Wasu ‘yan bindiga su 7 sun afka wa wani asibiti mai zaman kansa a lafia, babban birnin jihar Nasarawa a tarayyar Najeriya, inda suka yi awon gaba da mutane 5.

Talla

Wasu ‘yan bindiga su 7 sun afka wa wani asibiti mai zaman kansa a lafia, babban birnin jihar Nasarawa a tarayyar Najeriya, inda suka yi awon gaba daa mutane 5.

‘Yan bindigar sun kutsa asibitin ‘Kun Warke’ ne da ke unguwar Kan Tsakuwa a birnin Lafia, suka kame wasu mutane 4, ‘yan uwan wani mara lafiya da ke kwance a asibitin tare da wata ma’aikaciyar asibiti guda.

Daraktan asibitin, wanda tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar ne, Elisha Agwadu ya ce bai wuce minti 30 da barin asibitin ba ‘yan bindigar suka isa wurin da misalin karfe 8 da rabi na daren Asabar.

Kwamishinan al’adu da yada labaran jihar Nasarawa, Dogo Shama, wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin gas ashen Hausa na RFI ya ce ‘yan bindigar sun kira mai asibitin ta waya, inda suka bukaci ya ba su Naira miliyan 30 don ya fanshi ma’aikaciyarsa da suka sace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.