Najeriya

Ministocin kudancin Najeriya sun bukaci bincike kan zargin kisa a Lekki

Ministocin Najeriya da suka fito daga yankin kudu maso yamma sun bukaci gudanar da bincike kan zargin da ake yiwa sojoji na harbi a hanyar Lekki lokacin zanga zangar adawa da zargin cin zarafin da ake yiwa jami’an Yan Sanda.

Wasu masu zanga-zangar bacin rai kan cin zarafin da wasu 'yan sanda ke yi a Najeriya.
Wasu masu zanga-zangar bacin rai kan cin zarafin da wasu 'yan sanda ke yi a Najeriya. Temilade Adelaja/Reuters
Talla

Ministan ayyuka da gidaje Babatunde Fashola ya bayyana haka a madadin ministocin da suka fito daga yankin bayan wani taro a fadar shugaban kasa.

Fashola ya ce bayan ziyarar yankunan su da su ka yi kamar yadda shugaban kasa ya bukata domin ganawa da jama’a sun amince da bukatar gudanar da binciken domin shaidawa al’ummar kasa gaskiyar abinda ya faru kan lamarin.

Ministan ya kuma ce sun bukaci karfafa rundunar 'yan sanda da jami’an ta wajen ganin sun sauke nauyin da ke kan su na kare lafiya da dukiyoyin jama’a ta hanyar kula da lafiyar su da kuma basu kayan aikin zamani.

Ministocin da suka fito daga yankin sun hada da Otunba Adeniyi Adebayo da Olamilekan Adegbite da Sunday Dare da Omotayo Alasoadura da Adeleke Mamora.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI