Amurka-Najeriya

'Yan Najeriya 2 sun lashe kujerun Majalisar wakilan Amurka

Wasu masu kada kuri'a a Amurka.
Wasu masu kada kuri'a a Amurka. REUTERS/Go Nakamura

Yayin da ake dakon sakamakon zaben shugaban kasar Amurka, sakamakon zaben ya nuna yadda wasu 'yan Najeriya guda biyu suka lashe kujerun Majalisar wakilai a cikin kasar.

Talla

'Yan Najeriyar 2 sun hada da Esther Agbaje daga Mazabar Minnesota da ta yi takara a karkashin Jam’iyyar Democrat wadda ta samu kashi 74 da rabi na kuri’un da aka kada a mazabar ta da kuma Oye Owolewa daga mazabar Yankin Colombia wanda ya lashe kashi 82 da rabi na kuri’un da aka kada a mazabar sa.

Owolewa ya fito ne daga Omu-Aran da ke Jihar Kwara, kuma ya na rike da shaidar karatun digiri na 3 a bangaren harhada magunguna, yayinda Agbaje ke da digiri biyu a bangaren shari’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.