Najeriya

Sojin Najeriya 9 sun rasa ransu bayan da motarsu ta taka nakiya a Maiduguri

Wasu Sojin Najeriya yayin rangadi a Maiduguri.
Wasu Sojin Najeriya yayin rangadi a Maiduguri. AFP/SUNDAY AGHAEZE

Rahotanni daga Najeriya sun ce akalla sojojin kasar 9 sun rasa rayukan su sakamakon taka nakiya da motar su ta yi a yankin arewa maso gabashin kasar mai fama da rikicin Boko Haram.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya bayyana cewar an samu hadarin ne a Malam Fatori da ke kusa da iyakar Nijar a ranar litinin din da ta gabata, lokacin da motocin sojin ke jigilar abinci daga Maiduguri.

Rahotanni sun ce rashin kayan sadarwa ya hana labarin fitowa da wuri.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Sojojin ke taka nakiyar ba, wadda aka daddasa ko kuma aka bibbirne a karkashin kasa duk dai cikin yakin da ake na kawo karshen kungiyar ta'addanci ta Boko Haram da ke ci gaba da kisan jama'a a yankin arewa maso gabashin Najeriyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.