Boko Haram-Najeriya

Sojin Najeriya sun halaka mayakan Boko Haram 75 a wata guda

Wasu dakarun Sojin Najeriya.
Wasu dakarun Sojin Najeriya. STEFAN HEUNIS/AFP

Rundunar sojin Najeriya ta yi ikirarin cewa za ta murkushe sauran mayakan Kungiyar Boko Haram da na ISWAP daga maboyarsu da ke yankin arewa maso gabashin Kasar, bayan wasu jerin farmakinta na baya-bayan nan da ta hallaka tarin mayakan kungiyoyin biyu.

Talla

Ma'aikatar tsaron Najeriya ta ce a cikin wata guda dakarun Sojin da ke rundunar musamman ta ''Operation fire ball'' ta yi nasarar kashe mayakan Kungiyar Boko Haram da na ISWAP 75 a yankin arewa maso gabashin kasar, ko da ya ke itama ta yi rashin dakaru 3 da suka kwanta dama a arangamar baya ga wasu 4 da suka jikkata.

Daraktan ofishin yada labarai na ma'aikatar tsaron Kasar Brigadier janar Benard Onyeuko, ya ce tsakanin ranar 28 ga watan satumba zuwa ranar 31 ga watan Oktoban da ya gabata ne aka samu wannan nasara.

Mr Onyeuko ya ce Rundunar ta ''Operation fire ball'' bangare daya ne karkashin Rundunar operation lafiya dole da aka kafa dan kakkabe sauran 'ya'yan Kungiyar, ganin yadda sukayi kaurin suna wajen kai hare hare a arewa maso gabashin Najeriya.

Ma'aikatar tsaron ta Najeriyar ta ce yayin farmaki, Sojin sun yi nasarar kwato motoci masu dauke da bindigogi da tarin makamai, cikin su har da bindigogi kirar AK47 guda 10, na'urar harba bam din gurneti 4, bamabaman gurneti 36 da dai sauran makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.