Najeriya - Maiduguri

Zulum ya kulla yarjejeniya da jami'ar Al-Azhar don cigaban Barno

Gwamnatin jihar Barno a Najeriya ta kulla yarjejeniya da wasu jami’oin kasar Masar domin bunkasa harkokin kiwon lafiya a Jahar da kuma horas da dilibai.

Gwamnan Jihar Barno Babagana Zulum tare da shugabannin jami'ar Al-Azhar na Masar
Gwamnan Jihar Barno Babagana Zulum tare da shugabannin jami'ar Al-Azhar na Masar RFI hausa/Abba
Talla

Yarjejeniyar ta samu asali yayin wata ziyar da gwamnan jihar Farfesa Babagana Umaru Zulum ya kai birnin Alkahiran Masar, inda ya ziyarci kungiyar tsoffin daliban jami’ar Al-Azhar na duniya ranar Laraba.

Gwamna Zulum ya bukaci hadin gwiwa domin horar da malamai a manyan makarantun jihar Barno da masu wa’azi.

Gwamnan ya kuma bukaci bude Cibiyar Al-Azhar a Maiduguri chelkwatan jihar, wato sashin koyan harshen Larabci da kafa reshen kungiyar tsoffin daliban na Al-Azhar a jihar.

Zulum ya kuma ziyarci Jami’ar Ain Shams, ita ma a Alkahira, inda ya gana da Shugaban Jami’ar, inda suka tattauna batutuwa da dama da suka ta'allaka kan hadin gwiwa tsakanin Jami'ar da jihar Borno a fannin nazarin likitanci, akokarin sa na samar da samar da asibitin koyarwa na Jami'ar jihar ta Borno.

Farfesa Babagana Zulum, ya tattauna kan yiwuwar tura daliban koyan aikin likita zuwa kasar Masar, domin kwasa-kwasan da za su bada damar kwarewa a fannoni daban-daban na kiwon lafiya.

Bayan taron ganawar, an zagaya da gwamnan shashin horar da aikin likitanci da na kimiyya na jami’ar, inda ya samu cikakken bayanai game da shirye-shiryen da aka gabatar, wanda Zulum ya gamsu da fatan karfafa shirinsa na inganta Jami'ar jihar ta Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI