Wata sabuwar cuta na kashe matasa a Najeriya
Rahotanni daga Najeriya na cewa wata bakuwar cuta ta yi sanadin mutuwar sama da mutane 40 a jihar Enugu dake Kudu maso gabashin Najeriya.
Wallafawa ranar:
Wannan bakuwar cuta ta bulla ne a karamar Hukumar Igbo- Eze da ke jihar Enugu a kudu maso gabashin Najeria, kuma wasu kafafen yada labaran kasar sun ruwaito cewa an samu mace–mace a tsakanin al’ummomi 3, wato Umuokpu, Ete da Ogwurugwu a watan da ya gabata.
Ba a kai ga tantance dalilin mace–macen ba, amma mazauna garuruwan sun ce akasarin mamatan matasa ne, kuma sun yi fama da kasala ce da zazzabi da ciwon kai kafin su kai ga cikawa.
Kamar yadda wasu jaridun kasar musamman ta ‘The Cable ke cewa, babu wani jami’in gwamnati da ya tabbatar da wannan lamari a hukumance.
Wasu mazauna garin Umuokpu sun shaida wa manema labarai cewa, a kauyensu kawai, mutane akalla 5 sun mutu, yayin da a garin Ete, inda cutar ta samo asali, ta lakume rayuka fiye da 40.
Kungiyar matasan Igbo a yankin ta bakin shugabanta Solomon Onu sun bayyana takaici kan yadda hukumomi suka yi gum ba tare da daukar mataki a kan wannan mummunan al’amari ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu