Najeriya-Kaduna

Gwamnan Kaduna ya baiwa Sarkin Zazzau sandar mulki

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i yayin baiwa sabon Sarkin Zazzau sandar Mulki
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El Rufa'i yayin baiwa sabon Sarkin Zazzau sandar Mulki Nasir El Rufa'i

Gwamnan jihar Kaduna dake Najeriya Malam Nasir El Rufai, ya bukaci taimakon masu rike da Sarautar Gargajiya a matakai daban daban da su taimakawa gwamnati wajen taskace mutanen dake cikin yankunan su domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a cikin al’umma.

Talla

Yayin da yake jawabi wajen bikin mikawa Sarkin Zazzau na 19 Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, El Rufai yace suna bukatar alkaluman mutanen dake Jihar da abinda suke yi da kuma irin kayan more rayuwar dake wurin da kuma wanda ake bukata domin inganta rayuwar su.

Gwamnan yace duk da yake wasu yankunan jihar na fuskantar matsalolin tsaro suna daukar matakan da suka dace wajen bunkasa bangaren ilimi da kula da lafiyar jama’a da kuma samar da ayyukan yi, yayin da ya bayyana cewar kwarewar da Mai Martaba Sarkin Zazzau na 19 ke da shi wajen aikin gwamnati da kuma na jama’a zai taimaka masa wajen jagorancin Jama’ar Masarautar sa.

El Rufai ya kuma tabo muhimmancin Masarautar Zazzau wadda ta kwashe sama da shekaru 200 wajen bada ilimi da wayar da kai da kuma zaman lafiya tsakanin al’ummom daban daban, wanda yace sun zama al’adar Bazazzagi.

Gwamnan ya bayyana cewar Masarautar Zazzau ta dade tana kare wadannan muradu da suka shafi adalci da gaskiya da kuma amana, yayin da ya yabawa Marigayi Sarkin Zazzau na 18 Dr Shehu Idris wanda ya kwashe shekaru 45 a karaga, ya kuma samu shaidar adalci da amana da jagoranci na gari.

El Rufai sai ya bukaci Sabon Sarki Ahmad Bamalli da ya dora daga inda marigayin ya bari, musamman wajen hada kan jama’ar Masarautar baki daya.

Daga karshe Gwamnan ya bukaci Masu rike da Sarauta a Masarautar Zazzau da mutanen Masarautar da jama’ar Jihar Kaduna da su baiwa Sarkin goyan bayan da ya dace domin tabbatar da zaman lafiya a Jihar baki daya.

Dangane da wata sabuwar dokar da ta shafi Masarautun Gargajiyar Jihar kuwa, Gwamnan ya bayyana cewar za tayi cikkaen bayani kan Gidajen Sarautar da ake da su da kuma irin matakan da za’a bi wajen gadon ta a inda ake da gidajen sarautar da yawa da kuam ka’idodin nada Hakimai da Masu Unguwani da Majalisar Sarakunan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.